Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Alhamis Za A Rattaba Hannu kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Angola - 2002-04-04


Gwamnatin kasar Angola da 'yan tawayen UNITA, sun yi shirin rattaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wuta ta zahiri a yau alhamis, a wani kokarin kawo karshen yaki mafi dadewa kuma mafi muni a nahiyar Afirka.

Jami'ai sun ce shugaban kasar Angola, Jose Eduardo Dos Santos, da madugun UNITA na rikon kwarya, Paulo Lukamba, su ne zasu rattabawa yarjejeniyar hannu.

Wakilan kasashen makwabta da na Majalisar Dinkin Duniya, da Amurka da Rasha da kuma na Portugal, sune zasu halarci bikin rattabawa yarjejeniyar hannu.

A cikin watan jiya na Maris, aka fara yin tattaunawar kulla yarjejeniyar tsagaita wutar, bayan mutuwar Jonas Savimbi, dadadden madugun kungiyar UNITA.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta kumshi wani shiri na kwance damarar yakin 'yan tawayen UNITA.

Kungiyar UNITA ta fara yaki da gwamnatin kasar Angola kusan ba kakkautawa tun bayan da kasar Portugal ta baiwa kasar ta Angola 'yancin kanta a shekarar 1975. Yakin ya lankwame rayukan mutane akalla dubu 500.

XS
SM
MD
LG