Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankokin Isra'ila Sun Shiga Hebron - 2002-04-05


Shaidu sun ce tankoki da sojojin Isra'ila sun shiga birnin Hebron a yankin Yammacin kogin Jordan, a yayin da Isra'ila take fadada farmaki kan garuruwa da biranen Falasdinawa.

Tun kafin nan, sojojin Isra'ila sun riga sun kama birane da garuruwan Falasdinawa 6 a wannan farmakin da suka kaddamar mako guda da ya shige a kan 'yan kishin Falasdinu. Isra'ila ta ce ta kama Falasdinawa fiye da dubu daya a farmakin da ta kai cikin wadannan birane da garuruwa (Ramallah, Qalqiliya, Jenin, Tulkarem, Bethlehem da Nablus)

An bada rahoton fada mafi muni a Jenin, inda a jiya alhamis aka kashe Falasdinawa akalla 6 da sojojin Isra'ila 4.

Haka kuma ana ci gaba da yin cirko-cirko a tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawan da suka nemi mafaka cikin majami'ar "Church of the Nativity" dake Bethlehem. An ji fashe-fashe da karar bindigogi kusa da majami'ar jiya alhamis. Falasdinawa suka ce sojojin Isra'ila sun fasa kofa jikin bangon majami'ar, amma Isra'ila ta ce ba ta yi haka ba.

Wani babban jami'in Falasdinawa ya ce an kashe Falasdinawa fiye da 80 tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da wannan farmaki ranar Jumma'ar da ta shige. Isra'ila ta haramtawa 'yan jarida shiga dukkan yankunan da take gudanar da farmakin soja, a saboda haka babu waata kafar tabbatar da ikirarin Falasdinawan.

XS
SM
MD
LG