Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Sauran Kasashen Duniya Sun Yi Marhabin Da Tsagaita Wuta A Angola - 2002-04-05


Kasashen duniya sun yi marhabin da shirin tsagaita wutar da aka cimma da nufin kawo karshen yakin basasar da aka yi kusan shekaru 30 ana yi a kasar Angola.

A jiya alhamis Amurka da kasashe da dama suka yi marhabin da wannan yarjejeniya wadda gwamnatin Angola da kungiyar 'yan tawayen UNITA suka rattabawa hannu a jiyan.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje, Philip Reeker, ya ce Amurka tana zuba idanu domin ganin an kammala sauran matakan yarjejeniyar tsagaita wutar tare da cimma sasantawa a tsakanin al'ummar kasar. Ya ce a shirye Amurka take ta taimaka a wannan kokarin.

Britaniya, Faransa, Rasha, Sweden, da kuma Portugal wadda tayi wa Angola mulkin mallaka, duk sun yaba da shirin tsagaita wutar.

Babban mai bai wa Majalisar Dinkin Duniya shawara kan harkokin kasar Angola, mataimakin sakatare janar Ibrahim Gambari na Nijeriya, ya kalubalanci 'yan Angola da su tabbatar da cewa sun bai wa zaman lafiya damar dorewa.

Kwamandojin sojan Angola da na UNITA sune suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar jiya alhamis a Luanda, babban birnin Angola, a gaban manyan jami'an Angola da wakilan kasashen duniya. Kwamandan rundunar sojojin UNITA, Janar Abreu Kamorteiro, yayi alkawarin cewa sojojinsa zasu mutunta wannan yarjejeniya, zasu kuma mika makamansu.

Kungiyar UNITA ta yi ta yakar gwamnatin Angola tun lokacin da kasar ta samu 'yanci a shekarar 1975.

XS
SM
MD
LG