Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Afghanistan Sun Damke daruruwan Mutane Dangane da Makrkashiyar Kashe Shugaba Da Tsohon Sarkin Kasar - 2002-04-05


Hukumomin Afghanistan sun ce sun damke daruruwan mutane wadanda aka yi zargin suna da hannu a wata makarkashiyar da aka ce an kulla ta kashe shugaban gwamnatin rikon kwarya, Hamid Karzai, da tsohon sarkin kasar, Mohammed Zahir Shah.

Ministan harkokin cikin gida, Yunis Qanuni, ya kuma ce wadannan hare-haren bam da aka shirya kaiwa, zasu kuma shafi sojojin Amurka da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa dake Kabul.

Ya ce da farko an kama mutane 300 a birnin Kabul cikin 'yan kwanakin da suka shige, kuma har yanzu ana tsare da 160 daga cikinsu ana yi musu tambayoyi.

'Yan sandan Afghanistan sun ce akasarin wadanda aka kama, 'ya'yan kungiyar nan ce ta Hezbi Islami dake karkashin jagorancin tsohon firayim minista, Gulbuddin Hekmatyar, wanda ya fito fili ya bayyana adawarsa da kasancewar sojojin Amurka a Afghanistan. Amma jami'an kungiyar sun ce babu ruwan kungiyar da wannan makarkashiyar.

XS
SM
MD
LG