Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Dubatan Mutane Sun Yi Gangamin Goyon Bayan Falasdinawa - 2002-04-08


Daruruwan dubban mutane sun yi maci jiya lahadi a kasashe dabam-dabam na duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.

Wadanda suka shirya wani gagarumin gangami a Morocco, sun ce mutane fiye da miliyan daya suka yi maci a birnin Rabat domin yin tur da firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila da shugaba George W. Bush na Amurka. Jami'ai suka ce daruruwan dubban mutane suka halarci wannan zanga-zanga ta farko da hukumomi suka bada iznin gudanarwa tun lokacin da Falasdinawa suka fara tunzuri watanni 18 da suka shige. Manyan jami'an gwamnati sun shiga cikin wannan gangami na tsawon sa'o'i 5.

A Jordan, Falasdinawa sun gwabza da 'yan sanda a wani sansanin 'yan gudun hijira, a bayan da wani saurayi Bafalasdine ya rasu a sanadin raunin da ya samu a kai lokacin wata zanga-zangar nuna kin jinin Bani Isra'ila. Jami'an Jordan sun bada umurnin a gudanar da bincike.

A Bahrain, wasu daruruwan mutane sun yi ta rera taken "Allah Ya sa mu ga bayan Amurka, Allah Ya sa mu ga bayan Isra'ila" a lokacin da suke tafiya binne wani dan kasar ta Bahrain mai shekaru 24 da haihuwa, wanda ya mutu a sanadin raunin da ya samu a kai lokacin zanga-zanga ranar Jumma'a a kofar ofishin jakadancin Amurka a birnin Manama.

Wasu dubban 'yan zanga-zanga a kasar Musulmi mafi yawan jama'a, Indonesiya, sun kona tutar Isra'ila suka ringa rera baitocin nuna kyamar Amurka a lokacin ibada a birnin Jakarta.

Kamfanin dillancin labaran Reuta ya ce dubban 'yan zanga-zanga, da yawa daga cikinsu Falasdinawa, sun halarci tarurrukan nuna kin jinin Isra'ila a Beirut da sauran birane a fadin kasar Lebanon. Har ila yau, kamfanin dillancin labaran ya ce wasu 'yan zanga-zanga dubu 10 masu goyon bayan Falasdinawa sun yi maci jiya lahadi a titunan Brussels a kasar Belgium. Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ce an gudanar da irin wannan zanga-zanga a kasashen Sham(Syria), da Andalus(Spain) da kuma Misra.

A halin da ake ciki, wasu dubban mutane kuma sun yi maci a Paris da wasu biranen Faransa domin nuna goyon bayan Isra'ila tare da nuna rashin jin dadin hare-haren da aka kai cikin 'yan kwanakin nan kan cibiyoyin yahudawa a kasar. Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ce an soki wani dan sanda da wuka a ciki a lokacin da aka gwabza fada a tsakanin wasu kungiyoyi biyu na yahudawa masu gaba da junansu. Wannan gangami nasu ya zo kwana guda a bayan da dubun dubatan mutane suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a fadin kasar Faransa.

XS
SM
MD
LG