Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Mai Ya Cilla Sama A Bayan Da Iraqi Ta Tsayar Da Sayar Da Manta - 2002-04-09


Farashin man fetur ya cilla sama jiya litinin, a bayan da shugaba Saddam Hussein na Iraqi ya dakatar da sayar da mai ga kasashen waje, domin nuna rashin jin dadin farmakin da Isra'ila take kaiwa kan Falasdinawa.

Shugaba Saddam ya ce ya dakatar da sayar da man ne domin hukumta Isra'ila da Amurka, kuma zai yi hakan na kwanaki 30, ko kuma sai lokacin da Isra'ila ta janye daga yankunan Falasdinawa.

A halin da ake ciki, kasar Venezuela, wadda take tono mai fiye da kasar Iraqi, tana zaman jiran yajin aiki na gama gari da za a yi yau talata, wanda ke barazanar dakatar da dukkan harkokin mai a kasar tare da kara cilla farashinsa sama.

Babban sakataren kungiyar OPEC, Ali Rodriguez, ya bayyana damuwa da wadannan abubuwan dake faruwa, yana mai fadin cewa suna iya haddasa babbar matsala ta karancin mai.

Iraqi da Venzuela suna tono ganga miliyan 4 da rabi na mai a kullum, ko kuma kashi 6 cikin 100 na man duniya.

XS
SM
MD
LG