Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Dake Mulkin Zimbabwe Ta Gana Da 'Yan Adawa A Karon Farko - 2002-04-09


Jam'iyyar shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, ta tattauna a karon farko da 'yan adawa, tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya shige, wanda kuma ake ci gaba da yin gardama kansa.

Sassan biyu sun ce babu ci gaban da aka samu a tattaunawar da suka yi jiya litinin, amma kuma sun yarda zasu sake ganawa gobe laraba. Wannan shine karon farko da aka zauna wuri guda domin tattaunawa tsakanin jam'iyyar ZANU-PF da jam'iyyar adawa ta MDC, tun zaben shugaban kasa da aka gudanar daga ranar 9 zuwa ranar 11 ga watan Maris.

'Yan kallo masu zaman kansu sun ce akwai kuskure sosai a tsarin zaben. Mr. Mugabe yayi watsi da kiraye-kirayen gudanar da sabon zabe.

Masu fashin bakin siyasa sun ce shi da kansa ya bada umurnin wannan tattaunawa a saboda yana bukatar amincewar kasashen duniya kafin ya samo rance daga waje domin sayen abinci.

XS
SM
MD
LG