Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kara Nutsawa Cikin Biranen Jenin Da Nablus - 2002-04-09


Sojojin Isra'ila sun kara nutsawa cikin garuruwan Jenin da Nablus a yankin Yammacin kogin Jordan, wadanda Isra'ila ta bayyana a zaman tungayen Falasdinawa 'yan kishin Falasdinu.

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce wasu mayakan Falasdinawa sun mika wuya a Nablus, amma rahotanni daga bakin daga sun ce da alamun da yawa daga cikin 'yan kishin Falasdinu sun gwammace su mutu a wajen fada.

Har ila yau kuma, jirage masu saukar ungulu na Bani Isra'ila sun yi luguden wuta kan sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

A Bethlehem, an goce da musanyar wuta a tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawa a kusa da majami'ar "Church of the Nativity" inda Falasdinawa 200 suka nemi mafaka mako gudan da ya shige. Wani Bafalasdine a a cikin majami'ar ya ce sojojin Isra'ila sun bindige suka kashe wani dan sandan Falasdinawan da yayi kokarin kashe wutar da ta tashi a kusa da wannan wuri mai tsarki ga mabiya addinin Kirista.

A halin da ake ciki dai, 'yan sari-ka-noken Hezbollah dake Lebanon sun ce zasu ci gaba da kai hare-hare a tsallaken iyaka a kan sansanonin sojan Isra'ila. A jiya litinin, Isra'ila ta yi luguden wuta da jiragen saman yaki a kan wuraren da ake zaton na askarawan Hezbollah ne a wani martani na harin roka da suka kai cikin Isra'ila.

XS
SM
MD
LG