Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Tsaron Afghanistan Ya Tsallake Rijiya Da Baya - 2002-04-09


Wani bam ya tashi a tsakiyar 'yan kasar Afghanistan da suka yi layi domin yin maraba da ministan tsaro na rikon kwarya a birnin Jalalabad.

Mutane akalla hudu sun mutu, 18 suka ji rauni, amma kuma ministan tsaro Mohammed Fahim bai samu koda kwarzane ba, a wannan yunkurin da aka yi na kashe shi jiya litinin.

Mr. Fahim ya isa birnin na gabashin Afghanistan ne domin ya lallashi manoma su amince da shirin gwamnati na lalata gonakin zakami, babban sinadarin da ake amfani da shi wajen hada hodar iblis ta Heroin.

Jami'ai suka ce wata nakiya mai karfin gaske ta tashi kimanin mita 50 a gaban kwambar motocin ministan.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin. Amma jami'ai sun dora laifi a kan wadanda suka kira 'yan daba masu neman gurgunta kasar.

Manoma suna kukar cewa diyyar da gwamnati take son biyansu, ba ta kai wadda zata iya hana shukawa da noman zakami ba.

XS
SM
MD
LG