Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Hakki Tace Jami'an Tsaron Liberiya Suna Cin Mutuncin Jama'a - 2002-04-10


Kungiyar kare hakkin jama'a ta "Amnesty International" ta ce jami'an tsaron Liberiya sun tafka munanan ayyukan keta hakkin dan-adam, tun bayan da aka kafa dokar-ta-baci a kasar, watanni biyun da suka gabata.

Cikin wani rahoto da wannan kungiya mai hedkwata a birnin London ta fitar jiya talata, ta ce an samu karuwar ayyukan muzgunawa jama'a, wadanda suka hada har da yi wa mata fyade, da ganawa jama'a ukuba lokacin da jami'an tsaro suke yin sintiri a kasar.

Kungiyar ta ce, gwamnatin Liberiyar ta kasa kare farar hula daga samamen da jami'an tsaro suke kaiwa.

Kungiyar ta Amnesty ta kuma zargi shugaba Charles Taylor ta laifin kakaba dokar-ta-baci, domin ya murkushe kungiyoyin 'yanci da wayar da kan jama'a.

Amma ministan harkokin tsaron Liberiyar ya shedawa nan Muryar Amurka cewa, gwamnatinsa ta yi fatali da wannan rahoto, yana mai cewa kungiyar Amnesty ba ta yin la'akari da hatsarin da 'yan tawaye suke janyowa ga tsaron kasar ta Liberiya.

XS
SM
MD
LG