Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colin Powell Ya Ce Ya Kudiri Ganawa Da Yasser Arafat - 2002-04-10


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce ya kudiri ganawa da shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, wanda aka yi wa daurin talata, a wani bangare na ziyarar kokarin samar da zaman lafiya da ya je gabas ta tsakiya.

A tattaunawar da ya yi jiya a kasar Masar da shugaba Hosni Mubarak, Mr. Powell ya ce, zai sa himma domin yin dukkan abinda ya kamata, a kawo karshen rikicin Falasdinawa da Isra'ila. Sakataren harkokin wajen Amurkar, ya ce, a shirye yake, ya cigaba da tarewa a wannan yanki, domin karfafa himmar warware badakalar.

A can majalisar dinkin duniya kuma, kasashen larabawa suna zawarcin ganin kwamitin tsaro, ya bullo da wani sabon kudiri, wanda zai bukaci Isra'ila da ta janye daga biranen Falasdinawa. Amma Amurka ta ce, za ta ki amincewa da wannan kudiri, ta yi kira ga kwamitin tsaron ya dakata, ya ga sakamakon da ziyarar da Sakatare Powell yake yi yanzu za ta haifar.

XS
SM
MD
LG