Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai hari Kan Sojojin Afghanistan a Gabashin Kasar - 2002-04-10


Wani harin gurneti da aka kai kan wata kwambar sojojin Afghanistan mai yin sintiri da rufa-bayan dakarun Amurika a gabashin kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar soja daya, wasu kuma su bakwai suka jikkata.

Jami'an sojan Afghanistan sun ce wasu maharan da aka yi amanna cewa larabawa ne, sune suka jefa gurneti akan wata motar soja jiya talata. Sojojin Afghanistan sun mayar da wuta, suka kashe mutanen da suka kai farmakin.

Jami'an Amurka sun ce, ana nan ana rarraba wasu wasiku a gabashin Afghanistan, inda a ciki ake yin barazana ga mutanen dake marawa askarawan da Amurka take jagoranta.

Ba a san ko waye yake yin wannan barazana ba.

A jiya talatar ce kuma, shugaban gwamnatin wucin gadin Afghanistan din, Hamid Karzai, ya kai ziyara lardin tsakiyar kasar na Bamiyan, inda ya yi alkawarin bada cikakken 'yancin siyasa ga kabilar Hazara wadanda suka caba kazamin fada da 'yan Taleban.

An yi amanna cewa, wasu manyan kaburbura da aka gano kwanan nan a Bamiyan, suna kunshe ne da ‘'an kabilar ta Hazara, wadanda dakarun Taleban suka kashe.

XS
SM
MD
LG