Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bayan Da Falasdinawa Suka Kashe Sojojin Isra'ila 13, Sharon Ya Ce Zasu Ci Gaba Da Farmaki - 2002-04-10


Firayim Ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya ce kasarsa za ta ci gaba da kai farmaki a yankin Yammacin Kogin Jordan, har sai an dagargaza abinda ya kira "karikitan kungiyoyin Falasdinawa 'yan ta'adda."

Mr. Sharon ya furta haka ne jiya talata, bayan da aka kashe sojojin Isra'ila su 13 a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Dakarun na Isra'ila, sun fuskanci daga mai gauni a wannan sansani, inda jami'an Falasdinu suka ce an kashe Falasdinawa fiye da dari daya cikin makon da ya gabata.

A sauran wurare kuma, shaidu sun ce tankokin yakin Isra'ila da motocin rushe gine-gine, sun danna zuwa cikin yankin ikon Falasdinawa dake zirin Gaza. An bada rahotan cewa, sun dagargaza ofishin harkokin tsaron Falasdinawa.

A safiyar jiya talata ce, sojojin na Isra'ila suka janye daga biranen Tulkarem da Qalqiya dake yankin Yammacin Kogin Jordan. Amma kuma daga bisani sai suka mamaye birnin Dura, suka kama mutane masu yawa.

XS
SM
MD
LG