Mutane su akalla 10 sun mutu, yayin da wasu kimanin 20 suka ji rauni, a wani harin da a bisa dukkan alamu na kunar-bakin-wake ne da aka kai kan wata motar safa ta jigilar fasinja a kusa da garin Haifa dake arewacin Isra'ila.
'Yan sanda sun ce wannan dan harin kunar-bakin-wake ya tayar da bam a cikin motar wadda ke kan hanyar zuwa birnin Qudus.
'Yan sanda da ma'aikatan agaji suna wurin da wannan abu ya faru a yanzu haka.
Gidan rediyon Isra'ila ya ce dan harin kunar-bakin-waken ya tarwatsa wannan motar safa a wata mahadar hanya dake kusa da wannan birni mai tashar jiragen ruwa.
Wannan harin ya zo kwana guda a bayan da Falasdinawa suka yi kwanton-bauna suka kashe sojojin Isra'ila 13 a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.