Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Ya Ce Har Yanzu Yana Da Shirin Ganawa Da Arafat - 2002-04-11


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai sauka birnin Qudus a yau alhamis domin ganawa da firayim ministan Bani Isra'ila, Ariel Sharon, da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat.

Mr. Powell ya ce yana da muhimmanci gare shi ya tattauna da Malam Arafat, yana mai bayyana shi a zaman mai tasiri sosai a duk wani yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amma kuma Mr. Sharon ya ce duk wata ganawar da za a yi a tsakanin Mr. Powell da Malam Arafat "babban kuskure ne" a ta bakinsa.

Jiya laraba a kasar Andalus(Spain), Mr. Powell ya ce harin kunar-bakin-wake na larabar, da kuma kiyawar ad Isra'ila tayi ta kawo karshen farmakin da take kaiwa a yankin Yammacin Kogin Jordan, ba zasu gurgunta kokarinsa na ganin an samu cimma zaman lafiya ba.

XS
SM
MD
LG