Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Shiga Cikin Wani Garin Na Falasdinawa... - 2002-04-11


Sojojin Isra'ila sun sake shiga cikin wani garin na Falasdinawa a Yammacin kogin Jordan, 'yan sa'o'i kalilan bayan sun janye daga wasu kauyuka ukku.

Shaidu sun ce da jijjifin yau alhamis, tankokin yakin Isra'ila suka mirgina suka shiga Ber Zeit, suka kame garin ba tare da samun wata adawa ko turjiya ba.

A jiya laraba sojojin Isra'ilar suka janye daga kauyuka ukku bayan sun gama kakkabe Falasdinawa 'yan gwagwarmayar kwatar 'yancin kansu.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta yi marhabin da janyewar sojojin Isra'ilar, sannan ta yi kiran kasashen Larabawa da hukumar mulkin kan Falasdiwa da su yi tur da Allah waddai da hare-haren ta'addancin da ake kaiwa Isra'ila.

Tun da fari Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya gayawa gwamnatin Amurka cewa ta bar yi mishi matsin lambar lallai sai ya kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Yammacin kogin Jordan.

A jiya laraba wani Bafalasdine dan kunar bakin wake ya kashe 'yan Isra'ila takwas.

XS
SM
MD
LG