Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Dake Mulkin Afirka Ta Kudu Tayi Allah Wadarai Da Hukumcin Kotu... - 2002-04-12


Jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu, tayi tur da sallamar wani likitan zamanin mulkin wariyar launin fata, wanda aka tuhuma da laifin kisan kai, zamba da kuma fataucin muggan kwayoyi.

Kakakin ANC, Smuts Ngonyama, ya ce wannan hukumci da aka yanke jiya alhamis, babban abin bakin ciki da takaici ne. Ya ce ya sabawa duk wani tunani na da'a, a ce an saki Wouter Basson.

Masu gabatar da kara sun ce zasu daukaka karar wannan hukumci da aka yanke.

Alkalin babbar kotun Pretoria, Willie Hatzenberg, ya sallami Dr. Basson, wanda kafofin yada labaran Afirka ta Kudu suke kira "Likitan Mutuwa" ya kuma wanke shi daga dukkan laifuffuka 46 da aka tuhume shi da aikatawa.

Alkalin ya ce masu gabatar da kara ba su tabbatar da laifi ba tababa a kan likitan ba. Likitan mais hekaru 51 da haihuwa shi ma ya ce bai aikata wannan laifi ba.

daga cikin abubuwan da aka tuhume shi da aikatawa har da kulla makarkashiyar kashe sanannun abokan gabar gwamnatin wariyar launin fata ta hanyar ba su guba.

XS
SM
MD
LG