Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Kwango-Kinshasa Sun Yarda Da Kafa Rundunar Soja Guda... - 2002-04-12


Mashawartan gwamnati da na 'yan tawaye a zauren da ake shawarwarin neman aaman lafiya a Kwango-Kinshasa, sun yarda su hada dakarunsu cikin runduna guda, tare da kara wa'adin mako guda a tattaunawar da suke yi yanzu a Afirka ta Kudu.

Jiya alhamis tun farko aka shirya kawo karshen wannan tattaunawa ta birnin Sun City a Afirka ta Kudu, wadda ake yi da nufin kawo karshen yakin basasar kusan shekaru hudu.

Amma har yanzu wakilai a zauren taron ba su cimma daidaiton ra'ayi kan gwamnatin rikon kwarya ba. Kungiyar 'yan tawaye ta RCD ta yi fatali da wata shawarar da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya gabatar kan wannan. Shawarar tasa ta nemi a kafa majalisar mulkin kasa wadda zata kunshi shugabannin dukkan manyan kungiyoyin 'yan tawaye.

Har ila yau, shirin yayi kiran da shugaba Joseph Kabila ya ci gaba da rike mukaminsa, amma a matsayin na riko.

XS
SM
MD
LG