Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 6 Sun Hallaka Kusa Da Wurin Ibadar Yahudawa a Tunisiya - 2002-04-12


Wata tankar daukar mai tayi bindiga a wajen wani wurin ibadar yahudawa a tsibirin Djerba na Tunisiya, inda ta kashe mutane 6, ta raunata wasu kimanin 20 a jiya alhamis.

Shaidu sun ce wannan tanka ta hau kan dakalin gefen hanya ta doki katangar dake kewaye da wannan wurin ibadar yahudawa ta Ghriba, daga nan sai tayi bindiga.

Jami'an gwamnatin Tunisiya da shugabannin yahudawa na wurin sun ce wannan lamari dai hatsari ne. Amma wani jami'in diplomasiyyar Isra'ila ya ce wurin ibadar yana kan wata hanyar da ba a cika binta ba ne, abinda ke nuna cewa direban wannan mota ya bi wurin da gangan yana neman ginin ne.

Rahotanni daga Tunisiya sun ce wadanda suka mutu sun hada da wasu Jamusawa hudu 'yan yawon shakatawa da bude idanu, da direban tankar, da kuma wani dan sanda.

XS
SM
MD
LG