Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arafat Ya Ce Isra'ila Ta Wuce Makadi Da Rawa - 2002-04-12


Shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, yayi jawabi ta wayar tarho ga dubban mutanen da suka makare wata majami'a a Misra jiya alhamis, inda ya ce mamayar da Isra'ila tayi wa biranen Falasdinawa, ya wuce majkadi da rawa nesa ba kusa ba.

Malam Arafat yayi magana daga cikin gidansa a Ramallah, inda a yau makonni biyu cur ke nan sojojin Isra'ila suna kange da shi.

Ya bayyana farmakin Isra'ila a zaman cin zarafi da nuna fin karfi kan mata da yara da coci-coci da kuma Masallatan Falasdinawa.

Shugaban na Falasdinawa ya bayyana yadda sojojin Isra'ila suka yi wa majami'ar "Church of the Nativity" kawanya a Bethlehem, a zaman laifi.

Mutane akalla dubu biyu suka saurari wannan jawabi na Malam Arafat a birnin al-Qahira. Manyan malaman addinin Musulunci da manyan fada na Kiristocin darikar Coptic a Misra, duk sun bayyana goyon bayansu ga Malam Arafat da gwagwarmayar Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG