Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Ya Ce Sojojin Isra'ila Zasu Ci Gaba Da Zama a Biranen Falasdinawa Har Sai... - 2002-04-12


Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya ce sojojinsa zasu ci gaba da zama a garuruwan Falasdinawa har sai, a cewarsa, "'yan ta'adda sun yi saranda."

A jiya rundunar sojojin Isra'ila ta bada sanarwar cewa wai ta janye daga garuruwan Falasdinawa 24, amma kuma tankokin yaki da sojojinta sun kutsa cikin wasu sabbin garuruwan biyu a yankin Yammacin kogin Jordan da kuma wani sansanin 'yan gudun hijira.

Jami'an Falasdinawa sun bayyana sanarwar da Isra'ila ta bayar ta janyewa a zaman "shirga karya tsagwaronta" da nufin yin rufa ido wa duniya.

Har ila yau kuma, jami'an Isra'ila da na Falasdinawa suna bada labaran ad suka sha bambam da juna kan yawan Falasdinawan da aka kashe cikin makon nan a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin. Isra'ila dai ta ce mutane kimanin 100 ne suka mutu, amma wani jami'in Falasdinawa ya ce yawan wadanda Bani Isra'ila ta kashe zasu kai har 500.

XS
SM
MD
LG