Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jiang Zemin Na China Yana Nijeriya... - 2002-04-15


Shugaba Jiang Zemin na China yana ziyarar aiki a Nijeriya, da nufin habaka hadin kai tsakanin kasashen biyu.

Ana sa ran Mr. Jiang zai ganada takwaransa na Nijeriya, Olusegun Obasanjo, domin tattauna batutuwa da dama ciki har da siyasa, tattalin arziki da kuma fasaha.

A ranar asabar, Mr. Jiang ya ziyarci kasar Libya, inda ya gana da shugaba Mu'ammar Gaddafi.

Nijeriya ita ce zangon Mr. Jiang na uku a rangadin da yake yi a kasashe biyar. A bayan Nijeriya, zai ziyarci Tunisiya da Iran.

XS
SM
MD
LG