Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ethiopia da Eritrea Duk Suna Ikirarin Samun Nasara... - 2002-04-15


Ethiopia da Eritrea duk sun fito suna yin ikirarin samun nasara a hukumcin da kotun duniya ta yanke kan bakin iyakarsu da suka gwabza yakin shekaru 2 kai, har mutane kimanin dubu 80 suka sheka barzahu.

A Asmara, babban birnin Eritrea, ba a fito ana yin shagulgula kamar na Addis Ababa a Ethiopia ba, a bayan da Kotun Sasantawa ta Kasa da Kasa dake birnin Hague ta yanke hukumci ranar asabar.

Amma kuma dukkan kasashen biyu sun yi alkawarin mutunta hukumcin wannan kotu.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin Eritrea ta ce kawo karshen wannan yaki ta hanyar hukumcin kotu, nasara ce ga illahirin al'ummar Ethiopia da na Eritrea.

Amma kuma, sanarwar ba ta ce uffan ba a game da yankunan kasar da Eritrea zata maidawa Ethiopia, ko kuma wadanda za a maida mata.

Daga can daya gefen kuwa, Ethiopia tayi ikirarin cewa dukkan yankunan bakin iyakar da suke rikici a kai, misali Badme da kewayensa, da Zala Anbesa, da Aiga, ad Alitena da kuma gundumar Irob, zasu ci gaba da zama yankunan kasarta.

Jim kadan a bayan da aka yanke wannan hukumci a ranar asabar, ministan harkokin wajen Ethiopia, Seyoum Mesfin, ya ce Eritrea ta sha kashi a bakin daga, an kuma sake ba ta kashi a kotun shata bakin iyakar.

A jiya lahadi, dubban 'yan Ethiopia dauke da tutoci, sun yi ta buga ganguna, suna rawa suna waka a babban birnin kasar domin farin cikin wannan hukumci.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya bayyana hukumcin a zaman muhimmin ginshiki a shirin neman wanzar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG