Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jami'in Kula Da 'Yan Gudun Hijira Yana Nazarin Kokarin Da Ake Yi A Afghanistan - 2002-04-15


Babban jami'in kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Ruud Lubbers, yana kasar Afghanistan, a wani bangare na rangadin kwanaki takwas ad yake yi domin auna kokarin sake tsugunar da mutane da majalisar ke gudanarwa a yankin.

A jiya lahadi Mr. Lubbers yayi tattaki zuwa Afghanistan daga kasar Iran, inda ya ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira, ya kuma tattauna da shugaba Mohammed Khatami.

A lokacin da yake Afghanistan, ana sa ran Mr. Lubbers zai gana da shugaban gwamnatin rikon kwarya, Hamid Karzai. Har ila yau, Mr. Lubbers ya ce yana son ganawa da kasashe masu bada agaji domin neman tallafin kudin maida 'yan gudun hijiran Afghanistan su miliyan daya da dubu dari biyu gida a cikin wannan shekara.

Nan gaba cikin wannan mako zai zarce zuwa kasar Pakistan.

XS
SM
MD
LG