Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Colombiya - 2002-04-15


A Colombiya, Dan-takarar shugabancin kasar da yafi yin fice, Alvaro Uribe, ya auna arziki, bayan wani yunkurin kashe shi da aka yi.

Hukumomi sun ce wani bam ya fashe jiya lahadi, a kusa da wata motar safa, daidai lokacin da ayarin motocin Mr. Uribe yake barin wani wurin yakin neman zabe dake birnin Barranquilla.

Kodayake ya kubuta ba tare da yin ko da kwarzane ba, amma wasu mutane su uku dake bakin hanya sun mutu, wasu kuma akalla 20 suka jikkata.

Babu wanda ya dauki alhakin dasa wannan bam, amma rahotanni sun ce, mai yiwuwa za a zargi dakarun juyin-juya-halin kasar ta Colombiya.

Bayan alkawarin da ya yi na darfafar 'Yan-tawaye idan aka zabe shi, Mr. Uribe yana ci gaba da samun magoya baya, a kuriiun jin ra'ayoyin jama'a da ake gudanarwa, kafin zaben da za a yi ranar 26 ga watan gobe na Mayu.

Batun hare-haren mayakan sunkuru da na ta'addanci, za su kasance cikin al'amuran da shugaban Colombiyar mai barin gado, Andres Pastrana, zai tattauna da shugaba Bush ranar alhamis a nan birnin Washington, D.C.

XS
SM
MD
LG