Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yayin Da Falasdinawa Suka Ce 'A Kai Kasuwa' Ga Wani Tayin Isra'ila... - 2002-04-15


Wani lokaci a yau litinin, Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai yada zango a kasashen Syria (Sham) da Lebanon, domin ya tattauna a game da karuwar zaman tankiya ta fuskar soji a tsakanin Isra'ila da mayakan sunkurun Hezbollah dake Lebanon.

Mr. Powell zai gana da Firayim Ministan Lebanon, Rafik Hariri, da shugaban Syria, Bashar al-Assad, a daidai lokacin da ake nuna damuwa, cewa bisa la'akari da makonni da aka shafe ana harbe-ni-in-harbe-ka a tsakanin iyakokin Isra'ila, matsalar za ta iya kazancewa ta zama fagen daga na biyu, a rikicin da ake fafatawa yanzu a gabas ta tsakiya.

A jiya lahadi, jami'an Isra'ila suka ce Mr. Powell ya yi na'am da wani taron lumana na kasashen yankin da firayim Ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya gabatar.

A jiya din ne kuma, Sakatare Powell ya gana da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, wanda ya gitta sharudda gameda batun taron yankin, sannan ya jaddada bukatar janye sojojin Isra'ila daga yankin yammacin kogin Jordan nan take.

A halin da ake ciki kuma, jami'an Falasdinawa sun ki amincewa da sharadin da Isra'ila ta sanya, gameda batun mika-wuyar Falasdinawan nan masu dauke da makamai, wadanda aka yi wa kofar-rago a cikin majami'ar nan ta "Nativity" dake birnin Bethlehem. Isra'ila dai, ta bukaci wadannan mayakan sa kai su fuskanci shari'a a wata kotun sojinta, ko kuma su tafi gudun hijira na dindindin.

Ta daya gefe kuma, kotun kolin Isra'ila ta bullo da wani tsari, domin ta tabbatar ta gano sunayen Falasdinawan da aka kashe a sansanin 'yan hijira na Jenin, sannan a bizne su.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne, bayan zargin da jami'an Falasdinawa suka yi cewa, sojojin Isra'ila suna bizne jama'a farar hula a wazga-wazgan kaburbura, domin su lullube kashe-kashen da suka yi a wannan sansani, wani lamari da Isra'ila ta musanta.

Karkashin hukuncin da kotun Isra'ilar ta yanke, ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Cross za su taimakawa sojoji a wani shiri wanda za a aiwatar da hadin gwiwar dangin mutanen da aka kashe din.

XS
SM
MD
LG