Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yaba Wa Ethiopia Da Eritrea Kan Yarjejeniyar Bakin Iyaka - 2002-04-16


Amurka ta yabawa Ethiopia da Eritrea saboda amincewar da suka yi da hukumcin da kotun kasa da kasa ta yanke wanda ya shata bakin iyakar kasashen biyu, bayan da suka gwabza mummunan yakin shekaru biyu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Philip Reeker, ya ce daidaitawa a kan bakin iyakar, "gagarumin ci gaba ne a kokarin wanzar da zaman lafiya."

Mr. Reeker ya ce kasashen biyu sun dauki abinda ya kira "matakin samar da ci gaba wajen kulla cikakken zaman lafiya mai dorewa ta hanyar nuna karfin hali."

Har ila yau ya ce Amurka zata bai wa wani asusun Majalisar Dinkin Duniya na musamman da aka kafa karin kudi domin ya shata bakin iyakar Ethiopia da Eritrea.

A ranar asabar aka gabatarwa da gwamnatocin kasashen biyu hukumcin da Kotun Sasantawa ta Dindindin dake birnin Hague ta yanke.

Ministan harkokin wajen Ethiopia, Seyoum Mesfin, ya ce wannan hukumci nasara ce ga kasarsa a saboda ya tabbatar mata da mallakar dukkan yankunan da tayi ikirarin cewa nata ne.

Eritrea ba ta ce uffan ba a game da yankunan da zata mikawa Ethiopia, ko kuma yankunan da za a mika mata. Amma dukkan kasashen biyu sun ce zasu yi na'am da hukumcin kotun.

XS
SM
MD
LG