Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karzai Ya Doshi Rum Domin Rako Tsohon Sarkin Afghanistan Zuwa Gida - 2002-04-16


Ana sa ran shugaban gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan, Hamid Karzai, zai sauka yau talata a birnin Rum domin ya gana da tsohon sarkin Afghanistan, Mohammed Zahir Shah, kafin yayi masa rakiya zuwa gida.

Wannan shine karon farko cikin kusan shekaru 30 da tsohon sarkin zai taka kasar Afghanistan. An dauki tsauraran matakan tsaro, kuma ba a bayyana takamammen lokacin tafiyar ba.

A halin da ake ciki, ma'aikatar tsaron Amurka ta ce sojojin Amurka hudu sun mutu lokacin da albarusai suka yi bindiga jiya litinin a kusa da birnin Kandahar dake kudancin Afghanistan. Sakataren tsaro Donald Rumsfeld, ya ce wani sojan guda daya ya ji rauni a wannan lamarin.

A wani labarin kuma, gidan telebijin na al-Jazeera, jiya litinin ya watsa hotunan bidiyo na shugaban kungiyar al-Qa'ida, Osama bin Laden, da babban mukaddashinsa, Ayman al-Zawahiri. Sakataren tsaron Amurka, Rumsfeld, ya ce an fada masa cewa tsoffin faya-fayen bidiyo ne aka harhada wuri guda aka watsa.

XS
SM
MD
LG