Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Chavez Yayi Kiran A Yi Tattaunawar Sulhu Na Kasa - 2002-04-16


Shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya ce wani kwamitin bada shawara na gwamnati da zai gana yau talata, zai shirya tattaunawa ta kasa baki daya kan matsalolin dake addabar kasar.

Kwana guda a bayan da ya komo kan karagar mulkinsa, bayan wargajewar juyin mulki na ranar jumma'a, shugaba Chavez ya ce zai gayyaci mutane daga kowane bangaren akida a kasar Venezuela domin su zo su bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da suka shafi kasar.

Yunkurin juyin mulkin da aka so yi masa ranar Jumma'a ya biyo bayan yajin aiki na gidan kowa da shi da aka kaddamar da nufin goyon bayan ma'aikatan kamfanin mai na kasar wadanda suka fara yajin aiki suna neman a kori darektocin da shugaba Chavez ya nada a kamfanin. A yanzu, shugaba Chavez ya ce yayi na'am da takardun murabus din darektocin.

A halin da ake ciki, ma'aikatar harkokin wajen Amurka tayi kira ga 'yan Venezuela da su yi amfani da wannan dama domin tabbatar da sasantawa a tsakaninsu.

XS
SM
MD
LG