Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Ya Ce Isra'ila Zata Janye Sojojinta Cikin Mako Guda... - 2002-04-16


Firayim ministan Bani Isra'ila, Ariel Sharon, ya ce kasarsa zata janye sojojinta cikin mako guda daga dukkan biranen yankin Yammacin Kogin Jordan, amma ban da biranen Bethlehem da Ramallah.

Yayi wannan alkawarin ne cikin hirarrakin da yayi da wasu gidajen telebijin na Amurka jiya litinin. Har ila yau, yayi magana ta wayar tarho kan alkawarin janyewar da shugaba Bush, wanda ya bayyana wannan al'amari a zaman "matakin ci gaba."

Wannan shine karon farko da Mr. Sharon ya bayyana tsarin lokacin da Isra'ila zata kawo karshen farmakin da take kaiwa a kan Falasdinawa a Yammacin kogin Jordan. Isra'ila ta kaddamar da wannan farmaki ranar 29 ga watan Maris, bayan munanan hare-haren kunar-bakin-wake da Falasdinawa suka kai mata. A cewar Mr. Sharon dai, an kai farmakin ne da niyyar zakulo 'yan kishin Falasdinu.

A can wani gefen kuma, tankoki da sojojin Isra'ila sun sake shiga cikin garin Falasdinawa na Tulkarem. Majiyoyin soja na Isra'ila sun ce an kaddamar da sabon farmakin ne da nufin kamo 'yan ta'adda, ba wai don sake mamaye garin ba.

Wani babban jami'in Falasdinawa, Saeb Erekat, ya ce Mr. Sharon yana nuna halin ko oho da shugaba Bush na Amurka da kuma ra'ayoyin al'ummar duniya ta hanyar kin janyewa nan take daga Yammacin kogin Jordan.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai gana da Mr. Sharon nan gaba a yau talata. Ana sa ran mutanen biyu zasu tattauna wani ra'ayin da Isra'ila ta gabatar na kiran taron kolin Gabas ta Tsakiya wanda zai iya sake farfado da shirin samar da zaman lafiya.

Isra'ila tana son a yi taron ba tare da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat ba. Malam Arafat ya amince da ra'ayin gudanar da wannan taron, amma kuma Falasdinawa sun ce tilas sai Isra'ila ta janye daga dukkan birane da garuruwan Falasdinawa kafin a yi wannan taron.

Sakatare Powell ya bada shawarar ministocin harkokin wajen sassan su gudanar da wannan taro. Watakila Mr Powell zai gana da Malam Arafat gobe laraba.

A wani gefen kuma, ma'aikatan agaji na kasa da kasa, cikinsu har da Falasdinawa ma'aikatan jinya, sun gane wa idanunsu a karon farko irin barnar da aka yi wa sansanin Falasdinawa 'yan gudun hijira na Jenin. Falasdinawa sun zargi sojojin Isra'ila da laifin gudanar da kashe-kashen gilla cikin sansanin, inda suka ce an kashe daruruwan mutane, cikinsu har da fararen hula masu yawa. Isra'ila ta ce akasarin wadanda ta kashe 'yan bindiga ne, kuma ba su kai dari ba.

XS
SM
MD
LG