Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Zai Kammala Rangadin Gabas Ta Tsakiya Yau Laraba... - 2002-04-17


Wani lokaci a yau laraba, Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai gana da shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a abinda ake kyautata zaton ita ce ranarsa ta karshe, a ziyarar aikin da ya je Gabas ta Tsakiya.

Jiya talata, wani babban jami'in Falasdinawa ya ce, aikin samun zaman lafiyar da Sakatare Powell ya je yi wannan yanki bai cimma nasara ba, saboda bai iya tabbatar da cewa Isra'ila ta janye daga biranen Yammacin kogin Jordan da sauran alkaryu ba.

Babban magatakardar hukumar mulkin Falasindawa ta P-L-O, Malam Mahmoud Abbas, ya ce ba tare da janyewa ba, aikin Mr. Powell bai samar da wani sakamako ba.

A jiya talatar ce kuma, Sakatare Powell ya gana da Firayim Ministan Isra'ila Ariel Sharon. Mr. Sharon ya ce, wannan taro, ya fi mayar da hankali gameda wani taron koli na kasashen yanki, da ake kokarin yi, da nufin tada-injin tattaunawar zaman lafiya, a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG