Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Gana Da Firayim Ministan Lebanon Rafiq Hariri Yau... - 2002-04-17


A yau laraba shugaba Bush zai gana da firayim ministan Lebanon, Rafiq Hariri. Wakilin Muryar Amurka, Scott Stearns, ya ce ana sa ran mutanen biyu zasu tattauna wani shirin Sa'udiyya na kawo karshen fadan Gabas ta Tsakiya.

Ganawar da shugaba Bush zai yi da firayim ministan na Lebanon, kokari ne na rufa baya ma taron kolin kasashen Larabawa da aka yi a Beirut cikin watan da ya shige, inda shugabannin yankin suka amince da wani shirin Sa'udiyya na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Shirin ya tanadi cewa kasashen Larabawa zasu kulla hulda da Isra'ila idan har ta janye daga dukkan yankunan Larabawan da ta mamaye a yakin 1967. Wannan shiri, wanda Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya ya gabatar, ya samu goyon bayan Kasashen Tarayyar Turai da kuma Amurka.

Kakakin fadar White House, Ari Fleischer, ya ce shugaba Bush da firayim minista Hariri, zasu tattauna shirin na Sa'udiyya, da kuma abubuwan da za a iya yi a yanzu domin kusanto da sassan ga junansu.

Mr. Fleischer ya kuma ce mutanen biyu zasu tattauna hare-haren rokoki a tsallaken bakin iyakar Lebanon da Isra'ila inda Falasdinawa masu kishin Falasdinu suke ci gaba da kai raraka. Batun da ake takaddama kai shine na wasu gonakin da ake kira Shebaa wadanda Lebanon ta ce nata ne, amma kuma Isra'ila ta ce na kasar Syria ne. Sojojin Isra'ila suna ci gaba da mamaye wannan yanki, inda suka ce suna kokari ne na kare kai daga yunkurin Falasdinawa na fadada tashin hankalin dake faruwa a yankunan da Isra'ila ta mamaye ta hanyar bude bakin daga na biyu a tsawon iyakarta da Lebanon.

A mako mai zuwa, shugaba Bush zai gana da Yariman na Sa'udiyya a gidan gona da kiwon dabbobinsa dake jihar Texas domin tattauna shirin samar da zaman lafiyar, da kuma abinda Mr. Fleischer ya kira "tangarda" da aka samu a dangantakar Amurka da Sa'udiyya.

Yayin da yake bayyana cewa huldar dake tsakanin kasashen tana da karfi, kakakin na fadar White House ya ce koda yake kasashen abokai ne, ra'ayoyinsu sun sha bambam kan batutuwa.

Kafin ya gana da firayim ministan Lebanon, Rafiq Hariri, a yau laraba, shugaba Bush zai tattauna tashin hankali a gabas ta tsakiya da kuma yaki da ta'addanci a wata kolejin soja mai zaman kanta dake Jihar Virginia a kusa da nan birnin Washington.

XS
SM
MD
LG