Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwango Kinshasa Ta Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da 'Yan Tawayen Dake Samun Goyon Bayan Uganda - 2002-04-18


Gwamnatin Kwango Kinshasa da 'yan tawayen dake samun goyon bayan Uganda, sun yarda zasu kafa sabuwar gwamnati, amma kuma wata babbar kungiyar 'yan tawaye ta ki yarda da wannan shawara.

Jami'an Kwango suka ce a karkashin wannan yarjejeniya da aka rattabawa hannu jiya laraba a birnin Sun City, a Afirka ta Kudu, shugaban kungiyar 'yan tawaye ta "Congolese Liberation Movement", Jean-Pierre Bemba, zai zamo firayim minista. Sun kara da cewa shugaba Joseph Kabila zai ci gaba da zama a matsayinsa na shugaban kasa.

An bai wa kungiyar 'yan tawaye ta "Congolese Rally for Democracy" mai samun goyon bayan Rwanda ikon rike majalisar dokoki, amma ta yi watsi da wannan. Shugaban wannan kungiya da ake kira RCD a takaice, suna son a ci gaba da tattaunawa. Suka ce wannan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla ba zata dore ba, a saboda ta kunshi bangarori biyu ne kawai, ta bar sauran a gefe guda.

An cimma wannan yarjejeniya ana saura kwana daya kafin kammala taron kolin tattaunawa a tsakanin sassan kasar Kwango Kinshasa, wanda aka fara tun wajejen karshen watan Fabrairu a birnin Sun City.

An shirya tattaunawar da nufin kawo karshen yakin basasar Kwango Kinshasa. A makon jiya, shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya gabatar da wata shawarar da ta tanadi kirkiro da majalisar mulkin kasa da zata kunshi shugabannin manyan kungiyoyin 'yan tawaye biyu na kasar.

XS
SM
MD
LG