Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Sojan Kasar Netherlands Yayi Murabus... - 2002-04-18


Babban hafsan sojan kasar Netherlands yayi murabus, yayin da ake ci gaba da sukar cewa rundunar sojan kasar tayi rufa-rufa domin kare martabarta a bayan kisan gillar da aka yi wa Musulmi a Srebrenica, lokacin yakin Bosniya.

Janar Ad van Baal ya ce a yanzu ba zai iya kare muradun rundunar sojojin kasar ba, a bayan da aka wallafa wani rahoton da gwamnati ta dauki nauyinsa. Rahoton yayi tur da yadda sojojin kiyaye zaman lafiya 'yan kasar Netherlands suka kasa hana sojojin kabilar Sabiyawa kama wannan tungar Musulmi ta Srebrenica.

A ranar talata, gwamnatin hadin gambiza ta firayim minista Wim Kok tayi murabus a sanadin wannan rahoto.

Lauyoyin gabatar da kara a kotun shari'ar laifuffukan yaki ta kasa da kasa sun ce sojojin kabilar Sabiyawa sun kashe Musulmi maza manya da yara wadanda suka nemi mafaka a garin Srebrenica, wanda a lokacin Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a zaman tudun-mun-tsira.

XS
SM
MD
LG