Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi Sun Gurfanar Da Gwamnatin Amurka A Gaban Kotu... - 2002-04-18


An shigar da karar gwamnatin Amurka gaban kotu ana zargin cewa ta ci zarafin daruruwan Musulmi maza a lokacin da suke tsare bisa zargin karya dokokin shige da ficen baki, a bayan hare-haren 11 ga watan Satumba.

Takardar karar da aka shigar tayi zargin cewa an ci zarafin mutanen sosai ta hanyar gana musu azaba a lokacin da suke tsare a gidajen kurkuku a jihohin New York da New Jersey.

Har ila yau takardar karar tayi zargin cewa maimakon a dauke su a zaman marasa laifi har sai an tabbatar ad cewa sun aikata laifin, an dauki wadannan mutane a zaman wadanda suka aikata laifin ta'addanci har sai sun gamsar da hukumomin tsaro na Amurka cewa ba haka ba ne tukun.

Jiya laraba ne Cibiyar Kare Hakkokin da Tsarin Mulki ya tanada ta Amurka, ta shigar da wannan kara a madadin wadannan Musulmi da aka kama aka tsare.

XS
SM
MD
LG