Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Firayim Minista Hariri Na Lebanon Sun Gana A Fadar White House - 2002-04-18


Shugaba Bush da firayim minista Rafiq Hariri na Lebanon sun gana jiya laraba a fadar White House, inda suka tattauna halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Daga baya, firayim minista Hariri ya shaidawa 'yan jarida cewa ya matsa kan lallai Isra'ila ta janye daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye a yankin Yammacin kogin Jordan.

Ya ce ya kamata a dauki rangadin da sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya kai zuwa Gabas ta Tsakiya a zaman matakin fara wannan aiki.

Firayim minista Rafiq Hariri ya ce Lebanon tana son a cimma kammalallen zaman lafiya a yankin baki daya wanda zai hada da Lebanon da Sham(Syria) da kuma Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG