Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Zai Komo Ba Tare Da Cimma Tsagaita Wuta A Gabas Ta Tsakiya Ba - 2002-04-18


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai komo nan Washington, a bayan rangadin kwanaki goma a yankin Gabas at Tsakiya, inda ya kasa kulla tsagaita wuta a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Fadar White House ta ce nan gaba a yau alhamis Mr. Powell zai bayyana wa shugaba Bush sakamakon wannan rangadi nasa.

Shugaba Bush ya ce yayi imani Mr. Powell ya samu ci gaba a wannan rangadi nasa. A lokacin da yake magana jiya laraba a Jihar Virginia, Mr. Bush ya ce Amurka tana takalar wannan rikici da gaba na shekaru aru aru a tsakanin sassan yankin, amma ya ce zai ci gaba da kokarin ganin an samu zaman lafiya.

Kafin ya bar al-Qudus, Mr. powell ya ce kalmar "Tsagaita wuta" ba ta dace ba a yayin da Isra'ila take ci gaba da kai farmakin soja zuwa cikin yankunan Falasdinawa. Ya ce tilas Isra'ila ta kawo karshen wannan farmaki, kuma tilas shugabannin Falasdinawa su dauki matakan murkushe ta'addanci.

Mr. powell ya ce ya yarda da kalamun firayim ministan Isra'ila Ariel Sharon, cewar sojojin Isra'ila zasu janye daga yankunan da suka kama na baya-bayan nan a "wajejen mako mai zuwa."

A cikin sanarwar da suka bayar bayan da Mr. Powell ya tashi daga yankin, shugabannin Falasdinawa sun zargi Isra'ila da laifin toshe duk wata kafa ta cimma zaman lafiya. har ila yau sun yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, da ya tilasta yin aiki da kudurorinsa wadanda suka yi kira ga Isra'ila da ta janye nan take.

XS
SM
MD
LG