Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Yakin Amurka Yayi Kuskuren Jefa Bam Kan Sojojin Canada... - 2002-04-19


Wani jirgin saman yakin Amurka yayi kuskuren jefa bam kan wasu sojojin kasar Canada lokacin da suke yin atusaye ad sojojin Amurka kusa da birnin Kandahar a kudancin Afghanistan.

Jami'an sojan Canada sun ce an kashe musu sojoji hudu, wasu guda takwas kuma sun ji rauni, wasunsu mai tsanani.

Wani jami'in tsaron Amurka ya ce matukin jirgin ya sako wannan bam mai nauyin kilo 225 jiya alhamis, a bayan da ya zaci cewa harbe-harbe na gaskiya da yake gani a kasa ana auna shi ne domin a harbo shi.

Shugaba Bush ya buga waya ma Firayim Minista Jean Chretien na Canada domin yin jaje ga iyalan sojojin na Canada.

Sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld, ya bayyana takaici sosai kan wannan lamarin, ya kuma yi alkawarin bada cikakken hadin kai ga Canada wajen gudanar da binciken lamarin.

canada tana taimakawa sojojin Amurka da na Turai wajen farauto wadanda suka rage daga cikin kungiyar al-Qa'ida ta masu ta'addanci.

XS
SM
MD
LG