Wa'adin da hukumomin Yugoslaviya suka bai wa mutane 23 da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki yana karatowa cikin sauri. A ranar laraba ne hukumomins uka bai wa wadannan mutane wa'adin kwanaki uku na su mika kansu ko kuma a kamo su karfi da yaji.
Biyu daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa a jallo, watau tsohon madugun Sabiyawan Bosniya, Radovan Karadzic, da babban kwamandan sojojinsa, Janar Ratko Mladic, suna cikin jerin sunayen, tare da shugaban jamhuriyar Serbia na yanzu, Milan Milutinovic.
A jiya alhamis, babbar lauyar gabatar da kararraki a gaban kotun Shari'ar Laifuffukan Yaki ta MDD, Carla del Ponte, ta tattauna da jami'an Yugoslaviya a birnin Belgrade, domin matsa lambar da a mika mutanen dake tsare ko aka kama zuwa birnin Hague.
Hukumomin tarayyar Yugoslaviya sun buga jerin sunayen mutanen mako guda a bayan da majalisar dokoki ta zartas da dokar da ta bai wa gwamnati ikon mika mutanen da ake tuhuma zuwa kotun ta MDD.