Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Tayi Fatali Da Kiran Kofi Annan - 2002-04-19


Isra'ila ta yi fatali da kiran da Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya yi mata cewa, ta yarda a girke wata rundunar sojojin kasa da kasa a yankunan Falasdinawa, domin su taimaka a kawo karshen fadan da Isra'ilar take yi da Falasdinawa.

Jiya alhamis, mukaddashin jakadan Isra'ila a Majalisar dinkin duniya, ya gabatar da wannan sako ko kuma matsayi na Isra'ila, a daidai lokacin da kwamitin tsaron majalisar, ya fara yin muhawara gameda wani kudiri, wanda ya bukaci Isra'ila ta janye daga yankin yammacin kogin Jordan.

Jami'in diflomasiyyar na Isra'ila ya ce wata rundunar sojojin kasa da kasa ba za ta iya hana Falasdinawa mayakan sa-kai kaiwa Bani-Isra'ila farmaki ba.

Amma Mr. Annan ya yi nunin cewa, Isra'ila da Falasdinawa ba za su iya warware sabaninsu da kan su ba.

Ta daya gefe kuma, Falasdinawan da suka shaida al'amuran da suka wukana, sun ce tankokin yakin Isra'ila sun shiga birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza da jijjifin yau Juma’a, suka bude wuta, suka kashe akalla wani Bafalasdine daya.

XS
SM
MD
LG