Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Dubu 75 Suka Yi Zanga-Zanga A Washington... - 2002-04-21


Mutane har dubu 75 suka yi cincirindo jiya asabar a nan birnin Washington domin yin zanga-zangar batutuwa da dama, ciki har da goyon bayan da Amurka take bai wa Isra'ila, da kuma manufofin tattalin arziki na manyan kamfanonin duniya.

A wajen wani gangamin nuna goyon baya ga Falasdinawa da aka yi dab da fadar White House, masu zanga-zanga sun yi Allah wadarai da firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, suka kuma bukaci da lallai Amurka ta tilastawa Isra'ila ta fice daga cikin yankunan Falasdinawa.

Wasu 'yan zanga-zangar sun kwatanta Ariel Sharon da Adolph Hitler.

A kofar inda Bankin Duniya da Asusun Lamunin Kudi na Duniya suke yin taronsu kuma, 'yan zanga-zanga sun yi kira ga kasashe masu arziki ad su soke bashin da suke bin kasashe matalauta. 'Yan zanga-zangar suka ce cibiyoyin kudin suna fifita riba fiye da ukubar da jama'a ke sha, suka kuma yi kyalle da wani balo-balo mai tsayin mita 10, wanda aka zana taswirar duniya a jiki, aka kuma rubuta cewar "ta sayarwa."

Daga bisani, dukkan 'yan zanga-zangar sun hadu suka yi maci har zuwa farfajiyar majalisar dokokin Amurka. 'Yan sanda sun ce an gudanar da wannan zanga-zanga lami lafiya, kuma ba a kama ko da mutum guda ba.

An shirya gudanar da wasu zanga-zangar yau lahadi da kuma gobe litinin a nan birnin Washington.

XS
SM
MD
LG