Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cutar Shan Inna - 2002-04-22


Masu sauraro albishirinku:

Sashen Hausa na Muryar Amurka zai bada kyautar akwatunan rediyo akalla guda hudu, da riguna akalla guda ashirin. Abinda mai sauraro zai yi idan yana son samun kyauta daga cikin wadannan kyaututtuka, shine ya amsa wadannan tambayoyi guda hudu:

TAMBAYAR FARKO: Sau nawa ake bai wa yaro maganin rigakafin kamuwa da cutar shan inna kafin ya cika shekara guda?

TAMBAYA TA BIYU: Cutar shan inna daya ce kawai daga cikin cututtukan da ake iya yin rigakafinsu wa yara tun suna kanana. Fadi wasu cututtukan kuma guda uku da su ma ake iya yin rigakafinsu.

TAMBAYA TA UKU: A bayan cutar shan inna, wace allurar rigakafi ce ake yi wa yara idan sun kai makonni 6, da makonni 10 da kuma makonni 14 da haihuwa?

TAMBAYA TA HUDU: Digo nawa ne ake bai wa yaro idan an zo ba shi maganin rigakafin cutar shan inna?

A bayan wadannan tambayoyi, muna son a bayyana inda aka samo amsar kowace tambaya, ya Allah daga asibiti, ko hukumar lafiya, ko kuma dai wani wurin dabam.

A karshe kuma, muna son a kasa kowa ya rubuta mana sunayen shirye-shirye guda uku da ya fi so a Sashen hausa na Muryar Amurka.

Sai a yi sauri a rubuta amsoshin tambayoyin nan a jikin 'yar takarda mai kauri, watau Postcard, a aiko mana zuwa ga filin Gasar Cutar Shan Inna, sashen Hausa na Muryar Amurka, ta adireshin da aka saba. Zamu rufe karbar amsoshi a ranar 19 ga watan Afrilu, zamu kuma bayyana sunayen wadanda suka yi nasara ranar asabar 4 ga watan Mayu a shirinmu na safe.

Allah Ya bada mai rabo sa'a.

XS
SM
MD
LG