Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jimmy Carter Yayi Kiran Da Amurka Tayi Amfani Da Matsin Tattalin Arziki Kan Isra'ila... - 2002-04-22


Tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter, ya ce ya kamata Amurka tayi amfani da matsin tattalin arziki da na agajin soja a kan Isra'ila, domin tilasta mata janyewa daga yankunan Falasdinawa domin a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Mr. Carter, wanda ya shiga tsakani aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tarihi a tsakanin Isra'ila da Masar a 1979, ya rubuta cikin jaridar New York Times ta jiya lahadi, cewar a kowace rana, Amurka tana bai wa Isra'ila agajin kusan dala miliyan 10.

Tsohon shugaban na Amurka ya ce kokarin kawo karshen tashin hankali a Gabas ta Tsakiya ta hanyar diflomasiyya ya ci tura, a saboda haka yayi kiran da a sanyawa kasar Bani Yahudu matsin tattalin arziki.

Ya bayyana firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila a zaman mutum mai karfi da son nuna karfi. Ya ce yayi imani burin Mr. Sharon shine kakkafa unguwannin share-ka-zauna na yahudawa a duk fadin yankunan Falasdinawan da Isra'ila ta mamaye, ta yadda Falasdinawan ba zasu iay samun hadaddiyar kasa guda ba.

Mr. carter ya ce su ma Falasdinawan suna da nasu laifi, a saboda Malam Yasser Arafat bai taba murkushe kungiyar Hamas ko sauran kungiyoyin Falasdinawa da suka ki yarda da shirin yin zaman lafiya da Isra'ila ba.

XS
SM
MD
LG