Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zaben Majalisar Dokoki A Kasar Chadi... - 2002-04-22


Ana sa ran jam'iyyar da take mulkin kasar Chadi a yankin tsakiyar Afirka, cikin sauki zata lashe zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar jiya lahadi a fadin kasar.

'Yan kasar ta Chadi sun jefa kuri'unsu domin zaben sabbin 'yan majalisar dokoki 155, inda ake sa ran jam'iyyar Kishi da Ceto Kasa ta shugaba Idris Deby zata ci gaba da rike wannan majalisa.

Amma kuma masu jefa kuri'a kalilan suka fito, abinda masu fashin baki suka ce yana nuna rashin gamsuwa da zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar da ta shige. An yi ta zargin cewa an tabka magudi a wancan zaben.

A cikin makon nan ake sa ran za a fara samun sakamakon zaben, amma jami'ai sun ce za a dauki kimanin kwanaki goma kafin a samu cikakken sakamakon dukkan kujerun da aka yi takararsu.

A wannan zabe, an kara yawan kujerun majalisar daga 125 zuwa 155.

Masu fashin bakin siyasa sun ce abubuwan da suka dami masu jefa kuri'a a wannan karo a kasar ta Chadi, sun hada har da karuwar aikata miyagun laifuffuka, da rashin ayyukan yi da kuma irin rawar da mata zasu taka cikin siyasa da sauran harkokin yau da kullum na rayuwar dan Adam.

'Yan takara su fiye da 400 ne, cikinsu har da mata 35, suka yi takara a wannan zabe.

XS
SM
MD
LG