Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Ra'ayin Rikau Na Faransa Ya Hautsina Harkokin Siyasar Kasar... - 2002-04-22


Jagoran masu tsananin ra'ayin 'yan mazan jiya na Faransa, Jean-Marie Le Pen, ya haddasa hargowar siyasa a kasar, a bayan da ya sha gaba, ya kuma fitar da firayim minista Lionel Jospin mai ra'ayin gurguzu, daga zaben fitar da gwani na shugaban kasa da za a yi a wata mai zuwa.

Mr. Le Pen ya zo na biyu da kashi 17 cikin 100 na kuri'un da aka jefa a zagayen farko na zaben shugaban kasa jiya lahadi, ya shige gaban Mr. Jospin da kashi daya daga cikin 100.

Yanzu zai fuskanci shugaba mai ci, Jacques Chirac, mai ra'ayin rikau, wanda ya samu kusan kashi 20 daga cikin 100 na yawan kuri'un da aka jefa.

Jiya lahadi da maraice, firayim minista Jospin ya bada sanarwar cewa zai yi murabus daga harkokin siyasa. Jam'iyyar gurguzun tayi kira ga magoya bayanta da su goyi bayan shugaba Chirac a zaben fitar da gwanin na 5 ga watan Mayu, wanda ake sa ran Mr. Chirac zai lashe.

A halin da ake ciki, dubban mutane sun kwarara kan titunan biranen Faransa domin nuna rashin jin dadin yadda madugun masu tsananin ra'ayin rikau Le Pen ya zo na biyu a zaben.

A tarurrukan da aka yi a biranen Grenoble, Lyon, Strasbourg, da Toulouse, 'yan zanga-zanga sun bayyana rashin jin dadin ra'ayoyin siyasa na tsageranci na Mr. Le Pen.

Ministan kudi a gwamnatin Mr Jospin, Mr. Laurent Fabius, ya bayyana sakamakon zaben a zaman "bala'i mai tsoratarwa."

XS
SM
MD
LG