Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Ya Ce Sun Kammala Kashin Farko Na Farmaki A Yammacin Kogin Jordan - 2002-04-22


Firayim Ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya ce an kammala kashin farko na farmakin da kasarsa take kaiwa a yankin Yammacin Kogin Jordan, a daidai wannan lokaci da sojojinsa suke ci gaba da janyewa daga biranen Falasdinawa masu muhimmanci. Amma Mr. Sharon ya ce za a ci gaba da wannan farmaki wanda ya ce na kare-kai ne ta wani irin salo na dabam.

Bai dai yi karin bayani gameda abinda yake nufi ba.

Jami'an Isra'ila sun ce an kashe, ko kuma an damke 15 daga cikin Falasdinawa mayakan sa kai wadanda ake nema wurjanjan a kwanaki 23 da aka shafe ana kai wannan samame.

Isra'ila ta ce kodayake askarawanta suna daf da kammala janyewa daga biranen Nablus da Ramallah, amma za su cigaba da killace biranen da kuma hedkwatar shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, dake tsakiyar birnin Ramallah, da kuma cocin nan na "Nativity" dake birnin Bethlehem.

A halin da ake ciki kuma, Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce, ya yi murna da irin ci gaban da ake samu a batun janyewar Isra'ila daga yankin Yammacin kogin Jordan, amma kuma yana son ganin Isra'ilar ta sassauta killacewar da ta yi wa jagoran Falasdinawa, Yasser Arafat, ta ba shi wata dama da zai yi amfani da ikonsa.

Mr. Powell ya fadi haka ne jiya lahadi a shirin "Meet the Press" (Ganawa da 'yan Jarida) na gidan talebishan din NBC. Tun cikin watan disambar bara ne dai, aka yi wa Malam Arafat kofar-rago a helkwatarsa dake birnin Ramallah. A dangane da haka ne, Sakatare Powell ya ce, dole ne a samo wata hanyar shawartawa gameda lamarin, a kuma dakile kiki-kaka din da aka yi a cocin nan na nativity dake birnin Bethlehem.

XS
SM
MD
LG