Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Aikin Sake Kidaya Kuri'u A Kasar Madagascar - 2002-04-23


Babbr kotun tsarin mulki ta kasar Madagascar, ta fara aikin sake kidaya kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa na watan Disamba, wanda ya jefa wannan tsibiri na tekun Indiya cikin yamutsin siyasa.

Sake kidaya kuri'un, ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a kasar Senegal a makon da ya shige, tsakanin shugaba Didier Ratsiraka da Marc Ravalomanana, wanda ya ayyana kansa a zaman shugaba, wadanda kuma kowannensu ke ikirarin cewa shine mai mulkin wannan kasa mai mutane miliyan 15.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, idan har babu wani mutumin da ya lashe wannan zabe kai tsaye a bayan sake kidaya kuri'un, to za a gudanar da sabon zabe cikin watanni shida. Har ila yau, yarjejeniyar ta tanadi kafa gwamnatin rikon kwarya kafin a yi sabon zabe.

Jami'ai sun ce a cikin makonnin dake tafe kotun kolin zata bayyana sakamakon sake kidaya kuri'un zaben shugaban kasar.

Kasar Madagascar ta fada cikin mummunan rikicin siyasa tun lokacin da Mr. Ravalomanana, magajin garin Antananarivo, babban birnin kasar, kuma wanda yake da farin jini a wurin jama'a, ya ayyana kansa a zaman shugaban kasa a ranar 22 ga watan Fabrairu. Ya ki yarda da umurnin da kotu ta bayar na gudanar da zaben fitar da gwani yana mai cewa ya lashe wannan zabe kai tsaye a zagayen farko.

XS
SM
MD
LG