Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Kasar Colombia Sun Sace Gwamna, Da Tsohon Minista... - 2002-04-23


'Yan tawaye masu ra'ayin gurguzu a kasar Colombia, sun sace gwamnan wata jiha, da wani fada na coci da kuma tsohon ministan tsaron kasar, lokacin wani maci na neman zaman lafiya ta cikin yankin dake hannun 'yan tawaye.

Hukumomi sun ce an sace gwamnan Jihar Antioquia, Guillermo Gaviria, da fada Carlos Yepes, da kuma tsohon ministan tsaron kasar, Gilberto Echeverri, a lokacin ad suke yin maci tare da daruruwan mutane zuwa kauyen Caicedo a ranar lahadi.

Jami'ai suka ce 'yan tawayen kungiyar "Revolutionary Armed Forces of Colombia" sun sace wadannan mutane, a bayan da suka tsayar da masu macin na neman zaman lafiya domin yi musu tambayoyi game da aniyarsu.

Shugaba Andres Pastrana na Colombia, yayi tur da sace mutanen, amma kuma ya soki gwamna Gaviria saboda kin jin kashedin da sojojin gwamnati suka yi masa cewa akwai hadari kan hanyar.

Shugaba Pastrana ya fada jiya litinin cewa babu wani matakin tsaron da zai iya taimakawa muddin mutane suka yi watsi da shawarwarin rundunar soja.

XS
SM
MD
LG