Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Fita A Birnin Ahmedabad - 2002-04-23


'Yan sanda a Jihar Gujarat mai fama da fitina a kasar Indiya, suna yin sintiri a titunan wasu sassan birnin Ahmedabad, domin tilasta yin aiki da dokar hana fita, a bayan da aka samu karin tashin hankali mai muni tsakanin Musulmi ad 'yan addinin hindu.

An kashe mutane akalla 21 tun daga ranar Jumma'a. Daya daga cikinsu kuwa dan sanda ne wanda aka daba masa wuka. An kashe wasu 'yan zanga-zanga lokacin da 'yan sanda suka bude musu wuta.

Jiya litinin a birnin New Delhi, 'yan hamayya a majalisar dokoki sun tilasta ma dukkan bangarori biyu na majalisar sun dage zama a rana ta shida. Suna son gwamnati ta kori babban ministan Jihar Gujarat a saboda ya kasa shawo kan wannan tashin hankalin.

XS
SM
MD
LG