Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Isra'ila Da Na Falasdinawa Zasu Nemi Warware Cirko-Cirkon Majami'ar 'Nativity...' - 2002-04-23


Hukumomin Falasdinawa sun ce jami'ansu da na Isra'ila zasu gana yau talata domin su yi kokarin tattauna kawo karshen cirko-cirkon da ake yi a majami'ar Nativity dake Bethlehem.

Duk yunkurin da aka yi a baya na tattaunawa ya ci tura, inda bangarorin ke zargin juna.

Isra'ila ta bukaci sai lallai Falasdinawa 'yan bindiga dake cikin wannan coci su yi saranda. Har ila yau tayi alkawarin cewa ba zata kutsa da karfi cikin wannan coci ba, inda kiristoci suka yi imanin cewa an haifi Annabi Isa Alaihis Salam.

A can wani gefen kuwa, Falasdinawa sun ce Isra'ila ta kashe wani babban jagoran kungiyar 'yan Shuhada'u na al-Aqsa. Shaidun suka ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na Isra'ila ya cilla makamai masu linzami kan wata mota jiya litinin da magariba, inda ya kashe Marwan Zalloum da masu tsaron lafiyarsa.

Isra'ila ta dora masa laifin mutuwar yahudawa 'yan kama-wuri-zauna su 13.

A halin ad ake ciki, wakilan kasashen Larabawa sun shura takalmansu suka yi waje daga zauren wani taron ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai a kasar Spain, suka ki yarda da su saurari jawabin wani jami'in jakadancin Isra'ila.

Jami'an na Larabawa da Isra'ila sun je su Valencia a kasar Spain ne domin wani taron ciniki da tsaro tsakanin kasashen Tarayyar Turai da kawayensu dake bakin gabar tekun Bahar Rum.

A lokacin da mukaddashin ministan harkokin wajen Isra'ila, Michael Melchoir, ya mike domin yayi jawabi, jami'an Larabawa sun tashi suka fice daga zauren domin su nuna rashin jin dadin yadda Isra'ila take gallazawa Falasdinawa, da kuma yadda sojojin Isra'ila suka yi ma shugaban Falasdinawa Yasser Aarafat talala cikin hedkwatarsa a Ramallah.

Wasu jami'an jakadancin Turai sun ce wannan lamari ya nuna cewa tattaunawa tsakanin Isra'ila da Larabawa ba zata yiwu ba a wannan lokacin.

XS
SM
MD
LG